Tuesday, October 13, 2009

WANE IRIN ILIMI NE IDAN AKA ILIMANTAR DA `YA MACE KAMAR AN ILIMANTAR DA AL'UMMA NE?

WANE IRIN ILIMI NE IDAN AKA ILIMANTAR DA `YA MACE KAMAR AN ILIMANTAR DA AL'UMMA NE?
WANNAN ILIMI: Shi ne:Ilimin sanin Allah Madaukakin Sarki da sanin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam). Da sanin Addinin Musulunci, wannan shi ne ilimin da ya wajaba ga duk wanda Allah ya hore ma `ya mace ya ilimantar da ita wannan ilimi. Dole ne `ya mace ta san wannan kamar shi ma namiji dole ne akansa ya sani.
Dole `ya mace ta san yadda zata bautama Ubangijinta ta kowane yangare na dukkan abin da Allah Madaukakin Sarki yake so kuma ya yarda da shi, saboda mace da namiji dukkansu Allah ya dora musu nauyi na bin Shari'arsa kuma dukkansu zasu sadu da ukuba idan basu bi abin da ya ce ba kamar yadda Allah yake cewa a cikin Alkur'ani mai girma "Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan kwarai namiji ne ko mace, alhali kuwa yana Mumini, to, wadannan suna shiga Aljanna kuma ba za a zaluncesu ba gwargwadon hancin dabino ". Nisa'i: 124.

Daga nan sai sauran ayyukan da suka shafi (Ladubba) irin na Musulunci da mu'amala tsakaninta da wadanda Allah ya keye mata za ta yi ladabi da kuma sanin yadda zata yi zamantakewa tsakanin ta da iyayenta da mijinta da kishiyoyi da dai sauran wadanda Allah ya keye mata. Wannan shi ne kadan daga cikin irin ilimin da ya keyanci mace, wanda idan mace ta san wadannan abubuwa, to, shi ne kamar ka ilimantar da al'umma.

Sayanin kiraye-kirayen da ake yi ma mata cewar su fito su yi boko su yi aikin ofis, ko aikin watsa labarai, ko `yar sanda, ko sakatariya, ko tayi sarauta, ko wani abu makamancin haka, kenan suna nufin mata su fito su cakuda da maza ko suma suje kasuwa su kama shago suna kasuwanci kamar yadda maza suke yi, wadannan abubuwan da makamantansu basu halatta ga `ya mace ba a Addinin Musulunci, sai dai in son ran mu muke bi, ba Musulunci ba. Muna rokon Allah ya tsare mana Imanin mu, amin summa amin.

Shi dai Addinin Musulunci abin da ya tsara ma mace shi ne, ta zauna gidan mijinta ta bi shi sau da kafa yadda Allah ya umarce ta, kamar yadda Allah yake cewa "Kuma ku tabbata a cikin gidajenku kada ku yi tabarruji (shigar da bata dace ba) irin shigar `yan Jahiliyyar farko kuma ku tsaida Sallah kuma ku bayar da Zakka ku yi ma Allah da'a ku yi ma Manzon Allah da'a….". (Al-Ahzab:33).
Sannan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yana cewa a cikin Hadisin da Tirmizi da Abu Daura suka ruwaito yana cewa "Duk wanda yake da `ya'ya mata guda uku ko `yan'uwa mata guda uku ko `ya'ya mata biyu ko `yan'uwa mata biyu kuma ya yi musu ladabi ya kyauta musu ya aurar dasu, to, yana da Aljanna….". (Al-Hadith).

`Yan'uwa Musulmi wannan shi ne abin da Allah ya umarci duk wanda Allah ya hore na `ya'ya mata. Kuma sannan mu dubi irin busharar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yake yima duk wanda Allah yaba `ya'ya mata mu gani shin haka muke yi ko kuwa son ran mu muke bi?.

Daga karshe ina jawo hankalin `yan'uwa Musulmi akan cewar su daina ruduwa cewa yanzu ga wadanda ba Musulmai ba nan zaka ga matan su su suna hawa motoci ko suna da kudi da dai sauransu, ka sani kai a matsayin ka na wanda ya yi Imani, Allah yana gaya maka cewa "Kada jujjuyawar wadanda suka kafirata a cikin garuruwa ta rude ka. Jin dadi ne kadan sa'annan makomarsu Jahannama ce kuma tir da shimfida ita!". (Ali-Imran: 196-197). Kuma insha Allahu a fitowa ta gaba za mu ga irin sana'o'i da aikace-aikace da mata suka kasance suna yi zamanin Manzon Allah.

No comments:

Post a Comment