Kaskancin da aka jefa mata a ciki a wannan zamanin
Daga Baba Yola, Zariya
Alal hakika bayan doguwar wahala da gwagwarmayar da mata suka sha fama da ita har suka kwato kansu daga zalunci da kaskancin zamanin jahiliyya, wanda aka kaskantar da su a cikinsa, aka kuma zubar masu da mutunci tare da kwace masu ‘yanci, suka wayi gari suna mutane masu mutunci masu karimci da ‘yanci saboda albarkacin Musulunci da falalar jihadi da gwagwarmayar (wasu) mata, sai kawai ga shi su mata sun sake komawa kaskantattu, wulakantattu a wannan zamanin da suke ganin an ci gaba. Mutuncinsu ya sake fadawa cikin hadari saboda bin kaskantacciyar hanyar wannan zamani na yaudara. Har suka wayi gari tamkar kwandon sharar fasikanci, wadda maza ke zubar da sha’awarsu a ciki. Suka zamo kawai ababen wasa da morewa da kuma jin dadi. Siffarsu da hotunansu sun zama sune abubuwan kiran kasuwa da tallace-tallace.
An riga an karkatar wa mata tunaninsu zuwa ga al’amuran banza da wofi marasa kima, kamar su tallar kayan sa wa da na shafe-shafe da kwalliya, wanda a kansa zan yi tsokaci. Har ila yau babu shakka wannan hadari ne mai girman gaske, wanda yake barazana ga mutuncin mata da darajarsu, yake kuma neman ya mai da su mata tamkar haja wadda ake iya saya ko sayarwa bisa ga kyawu. Aka kuma karkatar da tunaninsu ba su komai sai tunanin kwalliya da shafe-shafe da gyaran gashi.
Anya kuwa mata a wannan zamanin za su iya fahimtar wannan sabon hadarin da ke fuskantar su duk da cewa an riga an lullube shi (hadarin) da kalmomi masu dadi, kamar soyayya ta hanyar yabo da bambadanci? Ko kuwa jefa kan nasu za su yi cikin cin mutunci da kaskanci da wulakanci?
Kai za ka ce ma galibin mata sun riga sun rudu da irin zantuttukan nan na kyal-kyal banza har sun fada cikin damuwa da wahala wadanda aka lullube da taken kwatar ‘yanci, ‘yan kalilan kam daga cikinsu sun riga sun farka, sun fahimci wannan sabon hadari, saboda haka suke kare daraja da mutuncinsu.
Zan dan gutsuro mana wani daga cikin zancen wata mashahuriyar marubuciyar Larabci a yayin da take bayanin irin hanyoyin da jahiliyyar wannan zamani ke amfani da su wajen kokarin sake mayar da mata cikin wulakanci da kaskanci.
Da aka tambaye ta me take gani game da mafi yawan mujallun nan da suke kiran kansu mujallun mata? Amsawa ta yi “Galibin wadannan mujallu ne na kwalliya wadanda ba su da wata manufa ga mace wadda ta shige rigunanta da akwamarta (akwati) da takalmanta. Sun mai da matan wannan zamani tamkar kwarkwaran dare dubu da daya.
“Irin wadannan mujallun sukan rika rubuta wa mata abubuwan shirme kamar ‘Me malamar za ta sa idan za ta fita shan iska bakin teku?’ ko irin rigar da za a sa da safiya, ko irin salon gyaran gashi na fita yammaci, ko kuma wace irin shiga za ki yi idan za ki ‘dina’?!
“Wato dai abin da mata za su sa da safe ya sha bamban da abin da za su sa da yamma. Wanda kuma za ta sa a gida daban ne da wanda za ta fita da shi. Wai bakin teku ma har yana da nasa tufafin na musamman!
“Wai mace ta kasance akalla tana da tufafin da za ta dinga sanyawa a koyaushe, kuma kowace riga ta kasance da abin wuyanta da ‘yan kunnenta, da janbakinta da zai dace da ita da takalma, tare da jakarta ko akwama. A takaice dai idan mace so take ta yi kwalliya kamar yadda wadannan mujalloli ke bukata daga gare ta, za ta ga cewa lalle rayuwar ma gaba daya ba za ta ishe ta kwalliya ba.!”
Wadannan kuwa duk kyale-kyalin banza ne, wanda maimakon ‘yan mata su mai da hankali wajen kara kaifin kwakwalwarsu da ci gaban dabi’u da kyautata halaye, sai ka iske su sun fi mai da hankali kan yawan tufafinsu da gyaran gashi. Kuma maimakon kokarin fadada tunani ta hanyar ilimi, sai yawon ballagaza da fasikanci da sanya dangalallun kaya, matsattsu wadanda za su bayyana gabobin jikinsu kamar kuyanga a kasuwar bayi!
Ta yiwu budurwa ta yi zaton cewa fitar da take yi tana bayyana jikinta wata walawa ce wadda ba za ta shafi tunaninta ba, saboda haka za ta iya kasancewa mai ‘yanci alhali tana kokarin bayyana wa jama’a adonta.
To a gaskiya a nan kam zan iya cewa kin yi kuskure, domin kuwa duk wani aiki da mutum yake aikatawa yana da tasiri mai dogon zango a cikin ruhinsa da kuma tunaninsa. Lalle ko shakka babu ayyukanmu suna da tasiri a kan tunaninmu. In ya zama tunaninmu ba shi ke tafiyar da tsarin rayuwarmu ba, to kuwa tsarin rayuwar namu zai zama shi ke tafiyar da tunanin namu.
Wani abu da ya kamata mu yi la’akari da shi shi ne cewa farkon sakamakon wannan gaye na je-ka-na-yi-ka, shi ne cewa yana kaskantar da mace ya kuma zubar mata da mutunci. Asasin wannan kaskanci kuwa shi ne kafuwar gyara a kan yawan tufafi da gyaran gashi, wanda kan sa mace jin cewa kyau wani abu ne, wanda rashinsa yana kaskantar da ita, ba wai abu ne da ta mallaka ba. Saboda haka idan dai tana so ta kasance kyakkyawa, sai ta yi matukar kokari dangane da hakan, ta yi aiki dare da rana domin cike gurbin nakasar da take da shi ga zatonta.
To muddin mace ‘yar gaye ce, wajibi ne ta mallaki tufafi masu yawan gaske tare da mahadansu wadanda ba su da iyaka. Ba wani abu ne boyayye a gare ku ba cewa gidajen kwalliya (saloon) sun riga sun kukkula wadannan abubuwa cikin almubazzaranci mai yawan gaske, yadda idan ma aka so a yi dan daidai-wadaida sai an kashe kudade masu dimbin yawa. Sa’annan kuma idan aka wayi gari aka samu manufar gaye ita ce a’ala a cikin al’umma, sai ya zama an haramta kyau ga matan talakawa. Yin haka kuwa zai sa kyau ya zama wani abin da sai masu dukiya za su iya mallakar sa kuma su yi masa babakere. A cikin wannan kuwa akwai kaskantarwa ga talakawa da fikirar ‘yan mata. A saboda haka gaye ya zama wani nau’i ne na nuna bambanci a al’umma.
Daga cikin barnar da wannan gaye na almubazzaranci ke yi wa mace ita ce barnatar da lokaci wanda yake shi ne hajar al’umma. Domin kuwa irin gayen da mujallun kwalliya suke kira a gare shi, yana bukatar lokaci wanda rayuwar mutum gaba daya ba za ta ishe shi ba. Da za ki tattara irin wadannan mujallun za ki tad da cewa abubuwan da mace take bukata domin ta kasance cikakkiyar ‘yan gaye rayuwar gaba dayanta ba za ta isa ba.
Sun kaskantar da wasu mata yadda har suka sa gyaran gashinsu ya zama wani abu mai wuyan gaske. Yadda sai ta je ‘Saloon’ an zaunar da ita a karkashin wani murhu na kusan awa biyu! Sun kuma farlanta mata shafe-shafen mai domin lausasa jiki na rabin awa kowace yamma da kuma minti goma sha biyar domin mikar da gashi. Haka nan kuma wajen gyaran kumba! Sannan kuma da wani lokaci na musamman domin kulawa da tafukan hannu da na kafa. Har ma da wani irin motsa jiki wai domin rage kugu!
Dukkan wadannan abubuwan suna dauke wa mace hankalinta su kuma cinye mata lokaci, yadda babu abin da zai sauara na ruhin mutuntaka a jikinta, sun mai da ita tamkar ‘yar bebi.
To za ta iya amfani da wannan lokaci da take batawa, wajen kula da nuna soyayya ga wani tsohonta mara koshin lafiya, ko wani takurarren miji nata, ko ma dai ta kula da wani jariri da yake bukatar kulawarta. Kuma maimakon lokacin da take batawa a ‘saloon’ tana iya karanta wani littafi wanda zai haskaka mata tunaninta ya kuma shiryar da ita.
Mata lokaci ya yi da za ku fita daga wannan kangi na tunani. Ku maza kuwa sai a tallafa masu wajen fadakarwa.
Tuesday, October 13, 2009
WANE IRIN ILIMI NE IDAN AKA ILIMANTAR DA `YA MACE KAMAR AN ILIMANTAR DA AL'UMMA NE?
WANE IRIN ILIMI NE IDAN AKA ILIMANTAR DA `YA MACE KAMAR AN ILIMANTAR DA AL'UMMA NE?
WANNAN ILIMI: Shi ne:Ilimin sanin Allah Madaukakin Sarki da sanin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam). Da sanin Addinin Musulunci, wannan shi ne ilimin da ya wajaba ga duk wanda Allah ya hore ma `ya mace ya ilimantar da ita wannan ilimi. Dole ne `ya mace ta san wannan kamar shi ma namiji dole ne akansa ya sani.
Dole `ya mace ta san yadda zata bautama Ubangijinta ta kowane yangare na dukkan abin da Allah Madaukakin Sarki yake so kuma ya yarda da shi, saboda mace da namiji dukkansu Allah ya dora musu nauyi na bin Shari'arsa kuma dukkansu zasu sadu da ukuba idan basu bi abin da ya ce ba kamar yadda Allah yake cewa a cikin Alkur'ani mai girma "Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan kwarai namiji ne ko mace, alhali kuwa yana Mumini, to, wadannan suna shiga Aljanna kuma ba za a zaluncesu ba gwargwadon hancin dabino ". Nisa'i: 124.
Daga nan sai sauran ayyukan da suka shafi (Ladubba) irin na Musulunci da mu'amala tsakaninta da wadanda Allah ya keye mata za ta yi ladabi da kuma sanin yadda zata yi zamantakewa tsakanin ta da iyayenta da mijinta da kishiyoyi da dai sauran wadanda Allah ya keye mata. Wannan shi ne kadan daga cikin irin ilimin da ya keyanci mace, wanda idan mace ta san wadannan abubuwa, to, shi ne kamar ka ilimantar da al'umma.
Sayanin kiraye-kirayen da ake yi ma mata cewar su fito su yi boko su yi aikin ofis, ko aikin watsa labarai, ko `yar sanda, ko sakatariya, ko tayi sarauta, ko wani abu makamancin haka, kenan suna nufin mata su fito su cakuda da maza ko suma suje kasuwa su kama shago suna kasuwanci kamar yadda maza suke yi, wadannan abubuwan da makamantansu basu halatta ga `ya mace ba a Addinin Musulunci, sai dai in son ran mu muke bi, ba Musulunci ba. Muna rokon Allah ya tsare mana Imanin mu, amin summa amin.
Shi dai Addinin Musulunci abin da ya tsara ma mace shi ne, ta zauna gidan mijinta ta bi shi sau da kafa yadda Allah ya umarce ta, kamar yadda Allah yake cewa "Kuma ku tabbata a cikin gidajenku kada ku yi tabarruji (shigar da bata dace ba) irin shigar `yan Jahiliyyar farko kuma ku tsaida Sallah kuma ku bayar da Zakka ku yi ma Allah da'a ku yi ma Manzon Allah da'a….". (Al-Ahzab:33).
Sannan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yana cewa a cikin Hadisin da Tirmizi da Abu Daura suka ruwaito yana cewa "Duk wanda yake da `ya'ya mata guda uku ko `yan'uwa mata guda uku ko `ya'ya mata biyu ko `yan'uwa mata biyu kuma ya yi musu ladabi ya kyauta musu ya aurar dasu, to, yana da Aljanna….". (Al-Hadith).
`Yan'uwa Musulmi wannan shi ne abin da Allah ya umarci duk wanda Allah ya hore na `ya'ya mata. Kuma sannan mu dubi irin busharar da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) yake yima duk wanda Allah yaba `ya'ya mata mu gani shin haka muke yi ko kuwa son ran mu muke bi?.
Daga karshe ina jawo hankalin `yan'uwa Musulmi akan cewar su daina ruduwa cewa yanzu ga wadanda ba Musulmai ba nan zaka ga matan su su suna hawa motoci ko suna da kudi da dai sauransu, ka sani kai a matsayin ka na wanda ya yi Imani, Allah yana gaya maka cewa "Kada jujjuyawar wadanda suka kafirata a cikin garuruwa ta rude ka. Jin dadi ne kadan sa'annan makomarsu Jahannama ce kuma tir da shimfida ita!". (Ali-Imran: 196-197). Kuma insha Allahu a fitowa ta gaba za mu ga irin sana'o'i da aikace-aikace da mata suka kasance suna yi zamanin Manzon Allah.

Subscribe to:
Posts (Atom)